Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Gwambe Ta Rufe Makarantu Da Suke Jihar Sakamakon Hare Haren 'Yan Binidga.


‘Yan sanda a wurin da bom ya fashe a Abuja 25,ga Yuni 2014.

A jihar Gombe hukumomi sun bada umurni rufe makarantun jihar na wani lokaci har sai ansamu yanayin tsaro mai inganci.

Rufe makarantun ya biyo bayan hare haren da yan bindiga ne suka kaddamar a garuruwan Nafada da kuma kamfanin yin siminti na Ashaka a jiya talata.

Rahotanni na nuni da cewar yan bindigan sun kashe wani shehin malamin nan Adamu Misra, da kuma almajiransa guda hudu a garin nafada, ayayinda suka kwashe nakiyoyi da motoci a kamfanin siminti na Ashaka.

Wani ma'aikacin kamfanin ne ya tabbatarwa wakilin Sashen Hausa Abdulwahab Mohammed haka, a hira da suka da shi.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG