Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Naija Ta Maida Martani Kan Hana Bara


Wadansu yara suna bara

Gwamnatin jihar Naija ta bayyana cewa, tana iyaka kokarinta na tallafawa makafin yadda ya kamata. Ta kuma ce, ana hana makafin bara a wadansu wurare ne domin kare mutuncinsu.

Gwamnatin jihar Naija ta Mayar da martani dangane da korafin da makafin jihar suka yi akan kama su da hukumomin jihar keyi.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa, tana iyaka kokarinta na tallafawa makafin yadda ya kamata. Gwamnatin ta kuma bayyana cewa, ba a ko’ina bane aka hana bara. Bisa ga cewar kwamishiniyar mata da nakasassu ta jihar, Hajiya Hassana Adamu, ana hana makafin bara a wadansu wurare ne domin kare mutuncinsu.

A cikin wani taron manema labarai da ta kira, kwamishiniyar tace an hana barace barace ne a manyan hanyoyin cikin garin Minna. Tace an ba makafin izinin zama wurare dabam dabam da suka hada da layin gidan sarkin makafi. Bisa ga cewarta, mabaratan zasu iya zama wajen gidan sarkin makafi da gidan kutare da kuma wani wuri dake Cancaga inda zasu iya zama wanda yake da niyar bada sadaka yaje ya neme su cikin mutunci.

Hajiya Hassana Adamu tace, gwamnatin jihar Naija ta kashe sama da Naira miliyan biyar wajen horas da makafi sana’oin hannu wadanda suka kamala aka basu takardun shaida da kuma kudin jari, banda haka kuma ana ci gaba da horas da wadansu a halin yanzu.

Isa Umar Aliyu shugaban hadaddiyar kungiyar makafi da ya halarci taron manema labaran yace abu daya da suke bukata a wajen gwamnatin jihar Naija a halin yanzu shine a yi masu rangwame a asibiti. Ya kuma yaba kokarin gwamnati na basu ilimi kyauta.

Wakilin Sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari ya ruwaito cewa, gwamnatin ta maida martanin ne sakamakon korafin da kungiyar makafi tayi kan kama su da gwamnati ke yi da kuma hanasu bara ba tare da basu tallafin kirki ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:00 0:00
Shiga Kai Tsaye
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG