Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Neja Ta Ce Ta Gano Wasu biliyoyin kudin Da Aka Wawure


Wasu daga cikin kudaden da aka yi ta bankadowa a gwamnatin Buhari

Kamar yadda wasu cibiyoyin gwamnati da jahohi su ka yi ta bankado kudaden sata, ita ma gwamnatin jahar Naija ta ce ta bankado.

Gwamnatin jihar Neja a Nigeria ta ce ta gano Naira milyan Dubu 6 da Milyan dari 2 na yan fansho da aka sace a jihar musamman daga ma’aikatan Kananan Hukumomi da Ma’aikatar Ilimi ta jahar. Yayin da hakan ke faruwa kuma Kungiyar Kwadagon jijhar ta koka kan rashin biyan hakkokin tsaffin Ma’aikatan da kudaden Paris kulop da jahar ta samu.

Mukaddashin Gwamnan jahar Alhaji Ahmad Muhammad Getso, wanda ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki kan batun fansho na jahar,ya ce an yi kwana da wadannan kudaden ne ta wajen fakewa da wani sabon tsarin fansho na jahar tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015, wanda y ace wannan ne babban dalilin da ya sa ‘yan fanshon jahar su ka shiga matsala.

To saidai kuma kungiyar Kwadagon jahar ta yi watsi da lamirin taron kwata-kwata. Ta ce hatta ita kanta gwamnati mai ci ta ki amfani da kudaden Paris Kulub wajen biyan hakkokin tsoffin ma’aita. Kwamrad Yahaya Idiris Ndku, Shugaban Kungiyar Kwadagon jahar ta Naija, ya ce an baiwa jahar kasonta na Paris Kulob har sau biyu amma ta ki biyan tsoffin ma’aikata hakkokinsu.

Ga Mustapha Nasiru Batsari da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG