Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Neja Ta Mayar Da Martani Game Da Kama Tsohon Gwamnan Jihar


Gwamnatin jihar Neja, ta mayar da martani a kan kamun da hukumar EFCC ta yi wa tsohon gwamnan jihar Dr Mu’azu Baban Gida Aliyu.

A lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a garin Muye, na yankin karamar hukumar Lapai, gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello, bai saki jiki ya yi wani dogon bayani ba akan lamarin, sai dai ya tabbatar da kamun tsohon gwamnan.

Ya ce, “Na karanta a jaridu dan haka ban san komi ba a kai, domon babu wani da ya gabatar mani da lamarin a hukumance” to amma daga bisani kwamishinan labarai na jihar Neja, Mr Jonathan Batsa, ya ce dama akwai korafe korafe da aka gabatar akan tsohon gwamnan.

Mr Jonathan, ya bayyana cewa akwai korafe korafe da dama da aka jingina a kan tsohon gwamnan wadanda a fili suke, amma tunda hukumar EFCC tana rike da shi, sai ta kammala binciken da ta ke yi, jama’a zasu ji cikakken lamarin da yayi dalilin cafke tsohon gwamnan.

Da aka nemi jin ta bakin sakataren yada labaran tsohon gwamnan ta wayar salula, Mr Israel Abije, ya bayyana cewa sai a ranar Juma’ar nan suke sa ran fitar da wata sanarwa a kan lamarin.

Mustapha Nasiru Batsari na da karin bayni.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG