Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Neja Ta Yi Shiru Kan Batun Karbo Kudaden Da Aka Sace A Baya


Dr. Babangida Aliyu tsohon gwamnan jihar Neja

Majalisar dokokin jihar Neja dake tarayyar Najeriya, ta nuna rashin gamsuwa da yadda gwamnatin jihar ke binciken kudaden da ake zargin jami’an tsohon gwamnatin da ta gabata da awon gaba da su.

Majalisar dai tayi wani zama ne na musammam a jiya Alhamis, inda mataimakin shugaban majalisar Hon Husaini Ibrahim Agaye, ya bankado wannan batu. A baya dai akwai makurden kudaden da sabuwar gwamnatin tace tsaffin jami’an gwamnatin sunyi awon gaba da su, amma har ya zuwa yanzu babu wani cikakken bayani kan maganar.

Daya daga cikin yan majalisar Hon Malik Madaki Boso, yace a yau kimanin watanni takwas da rantsar da wannan gwamnati, amma har yanzu batayi komai kan wannan batu ba, duk da yake in aka duba daga gwamnatin tarayya zuwa sauran jihohi kowa na bin diddigin duk wanda suka saci kudi ana karbowa, sai ga shi gwamnatin Neja tayi shiru.

Sai dai majalisar ta bayyana matsayinta na ganin an hukunta duk wanda aka samu da laifin wawure kudaden jama’a a baya.

Gwamnatin jihar dai ta mayar da martani kan wannan matsayi na yan majalisar, ta hanyar sakataren yada labarun gwamnan jihar Neja, Jibrin Baba, inda yace baki daya daga yan majalisar zuwa mutanen jihar zasu ga mamaki kan wannan maganar, ya kuma ce ana nan ana bincike har an kirawo wasu sun bayar da bayanai amma bai ambaci sunan kowa ba.

Masu nazarin al’amura na ganin cewa da wuya binciken yayi wani tasiri, musammam yadda ganin irin dangantakar da take tsakanin tsohon gwamna Babangida Aliyu, da kuma gwamnan na yanzu Alhaji Abubakar Sani Bello.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG