Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin jihar Niger ta hana a sayar da raguna akan tituna birnin Minna.


Rago
Rago

Gwamnatin jihar Niger ta haramta sayar da raguna a manyan titunan Minna baban birnin jihar. Tace ta dauki matakin ne a saboda dalilai na matakan tsaro

Hukumomi a jihar Niger, arewa maso yammacin Nigeria sun haramta sayar da raguna laiya akan manyan titunan Minna baban birnin jihar da kuma a harabar wasu ma’aikatun gwamnatin jihar.

Gwamnatin jihar Niger tace ta dauki matakin ne domin magance matsalar tsaro da kuma shawo kan matsalar satar raguna da ake samu a daidai irin wannan lokaci da babar sallah ke karatowa. A gefe guda kuma domin tsaftace birnin na Minna.

A duk shekara akan samu hada hadar cinnikin raguna saboda al’ummar Musulmi dake saye domin yanka a lokacin babar sallah.

Yusuf Inuwa Fuka, shugaban karamar hukumar Chanchaga, wadda ta kunshi cikin birnin Minna, ya yiwa wakilin sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari bayanin dalilinsu na daukan wannan mataki

Su kuma shugabanin kungiyar masu sayar da raguna, sunce basu da hannu a wannan sabuwar doka da gwamnatin jihar Niger ta kafa. Amma suna goyon bayan matakin hana sayar da raguna a bakin wasu ma’aikatun jihar.

Akasarin masu sayar da raguna a gefen titunan da harabar wasu ma’aikatun gwamnati, baki ne, wadanda suke zuwa daga wasu jihohin Nigeria. Daya daga cikin irin wadannan mutane mai suna Mallam Adamu Lawali, yace suna neman ahuwa tunda ba’a taba samun wata matsala daga bangarensu ba.

Gwamnatin jihar Niger tace ta ware wani makaken filli domin masu sayar da raguna.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG