Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya ta Dauki Mataki na bai daya domin yakar cutar Ebola


Shugaba Goodluck Jonathan
Shugaba Goodluck Jonathan

Gwamnatin taraiyar Najeriya,ta bayana cewa yanzu cutar nan ta Ebola ta bazu zuwa jihar Enugu, inda aka killace mutane 21 daga cikin mutane 197 da ake zatun cewa suna dauke da wannan cutar.

Wadannan mutane 197, an gano cewa sun yi ma’amala ko ta kai tsaye ko ta nesa da dan kasar Liberia nan da ya mutu da wannan cutar a cikin Najeriya.

Saboda mahimmanci da kuma dawainiyar wannan cutar ne yasa tuni gwamnatin taraiyar Najeriya, tayi taro na majalisar ministocin ta da kuma gwamnoni a Abuja domin hada kai domin tabbatar da cewa an dauki matakai na bai daya domin yakan cutar.

Sai dai gwamnatin Najeriya, tana alfa’ari da cewar a duk duniya babu wani dan Najeriya, dake dauke da wannan cutar inda ba wadan nan mutane dasu kadai ne suka yi ma’amala da Mr. Patrick Sawyer, wanda shine ya kawo cutar Najeriya, da har a kayi ma’amala dashi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:48 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG