Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Fara Shirin Gyaran Idanun Mutane Kyauta


Shugaba Goodluck Jonathan
Shugaba Goodluck Jonathan

A wani yunkuri na rage ciwon ido gwamnatin Najeriya ta fara wani shirin gyara idanun mutane kyauta

Gwamnatin Najeriya ta fara yiwa wasu mutane dari biyar masu lallurar idanu gyaran idanunsu kyauta.

Ta fara shirin ne a jihohin Oyo da Osun. Shirin mai lakabin mayarda da gani ga wadanda suke da matsalar idanu na Goodluck Jonathan za'a yi kwanaki biyar a na gudanarwa.

Mai shugabancin shirin Uwargida Abolanle Oyegoke ta ce an tsara shirin ne domin taimakawa 'yan Najeriya masu fama da matsalolin idanu. Dr Funke Ajoloko tana daya daga cikin likitoci masu gyaran idanun. Ta ce wasu masu gyaran idanu na gargajiya suna jawo matsala yayin da suke anfani da tsinke su soke wajen dake gani a cikin ido musamman idan cutar yanar ido ce. Yin hakan yana yiwa ido la'ani ya kuma lalace har ya kaiga makanta. Sabili da haka ta bukaci wadanda suk da matsala da idanunsu su guji yin anfani da maganin gargajiya.

Wasu da aka yiwa gyaran idanu sun bayyana ra'ayoyinsu. Sun roki gwamnati ta kara
kwanakin yin gyaran idanun saboda yawan jama'a. Wata ta ce lokacin da ta ga bata iya karatu sosai da ta ji batun gyaran idanu shi ya sa ta kawo kanta. Sabili da haka ta godewa shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Ana zaton za'a cigaba da gyaran idanu kyauta da bayar da magunguna zuwa sassan yankunan Najeriya.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:49 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG