Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Tace Tana Nazarin Ci Gaba Da Aikin Madatsar Ruwan Kafin Zaki Dam


Dam
Dam

Bayan da cece-kucen siyasa ya dakile aikin Madatsar ruwa ta Kafin Zaki Dam dake Jihar Bauchi tsawon kwashe shekaru da dama, a yanzu Gwamnatin Najeriya tace tana nan tana nazari akan yadda za a ci gaba da aikin, a kokarinta na bunkasa ayyukan noman Rani a kasar.

An tsara madatsar ruwa ta Kafin Zaki ne da nufin samar da ruwa ga manoman rani a sassan jihar Bauchi da Yobe da ma wasu bangarori na jihar Borno. Madatsar dai na daga cikin jerin Madatsun ruwa 12 dake karkashin kulawar hukumar kula da koramin Hadejia da Jama’are mai helkwata a birnin Kano.

Yanzu haka dai gwamnatin Tarayya tace tana jiran rahotan kwamitin kwararru game da wannan aiki na Kafin Zaki Dam, wanda zai bata damar sanin inda aka kwana a cewar ministan albarkatun ruwa Injiniya Sulaiman Husaini Adamu.

Samun nasarar wanzuwar madatsar ruwan Kafin Zaki Dam zai kara habaka ayyukan hukumar kula koramin Hadejia da Jama’are inji shugaban hukumar Sanata Mas’ud El Jibrin Doguwa, wanda yace idan anyi mutane dayawa zasu samu cin moriyar ta.

Saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

XS
SM
MD
LG