Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamantin Najeriya Tace Zata Hukumta Duk Masu Kalamun Batanci


General Abdulrahaman Dambazau, Ministan Cikin Gida
General Abdulrahaman Dambazau, Ministan Cikin Gida

Gwamnatin Najeriya, ta bakin ministan cikin gida Janar Dambazau zata yaki duk masu kalamun batanci da suka kusan zama ruwan dare gama gari da ake furtawa cikin wakoki, radiyo da kafofin sadarwa na zamani

Cikin 'yan watannin nan aka fara samun kalamun batanci da suka sa gwamnatin tarayya da hukumominta suka tashi tsaye domin yayyafa ruwan kwantar da kura.

Yunkurin gwantar da kurar ta hada da yadda Mukaddashin Shugaban kasa Farfasa Yemi Osinbajo da Ministan cikin gida Janar Abdulrahaman Dambazau da minstan yada labarai da daraktocin gidajen yada labarai da na wayar da kawunan jama'a suka tashi tsaye domin kalamun batanci, al'amarin da yanzu yake cikin karensa babu babbaka.

Dangane da matakin da gwamnatin tarayya ke tunanen dauka Janar Dambazau yana mai cewa "Musabbabin matakan da zamu dauka shi ne muka soma yanzu. Duk wanda muka samu yana kawo wadannan kalamun batanci ko na wakoki, ko wanda aka fadi a taro, kowane irin kalamai ma in dai kalamai ne na batanci, kalamai ne na jawo fitina, kalamai ne na jawo tashin hankali, kalamai ne wadanda zasu ingiza jama'a na yaki, na bullo da fitina to gaskiya za'a dau mataki mai tsanani a kansu kuma za'a gurfanar dashi gaban alakali ba wai babu shari'a ba ne. Akwai".

Ministan ya kara da cewa ba koyaushe ba ne gwamnati take son kama kwani yayi laifi saboda ana son a zauna lafiya wanda kuma idan babu shi ba za'a samu inganci rayuwa ba ,injishi.

Irin salon da kamalun suka dauka gano masu yinsu ka iya zama wata babbar matsala. Dr. Garba Abari daraktan hukumar wayar da kawunan jama'a yace suna da matakan da zasu dauka. Yana mai cewa gwamnati tana da hanyoyi da yawa da zata binciko asalin kowane kalamu da manufofinsu. Inji shi yanzu gwamnati ta yi nisa wajen zakulo asalin kafofin dake yada kalamun batanci da cin zarafi da suke fitowa kuma wai ta dauki matakai da yawa na tabbatar da cewa mutanen da basa son kasar da alheri basu ci nasaraba.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG