Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Zata Tattauna Da Boko Haram


'Yan kwana-kwana su na kokarin kashe wutar da ta tashi a hedkwatar 'yan sandan Najeriya a Abuja, bayan harin da aka ce 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai.
'Yan kwana-kwana su na kokarin kashe wutar da ta tashi a hedkwatar 'yan sandan Najeriya a Abuja, bayan harin da aka ce 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai.

A bayan da ya tattauna da shugabannin yankin da abin ya shafa, shugaba Goodluck Jonathan ya kafa kwamiti mai wakilai 7 domin tattaunawa da 'yan Kungiyar Boko Haram

Gwamnatin Najeriya ta ce tana son tattaunawa da kungiyar nan da aka fi sani da sunan Boko Haram, wadda aka dora wa alhakin kashe-kashe da dama a yankin arewa maso gabashin kasar.

Wata sanarwar gwamnati ta ce shugaba Goodluck Jonathan ya nada kwamiti mai wakilai 7 domin fara tattaunawa da kungiyar. Sanarwar ta ce shugaban ya nada wannan kwamiti a bayan da ya gana da shugabannin yankin da ake fama da wannan tashin hankali.

Har yanzu ba a ji martanin kungiyar game da wannan batun na tattaunawa ba.

Wannan shawara ta bude tattaunawa da kungiyar Boko Haram ta biyo bayan karuwar tashin hankalin da ya fi tsanani a Jihar Borno na arewa maso gabashin kasar, musamman Maiduguri babban birnin Jihar.

Kwanakin baya kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta ce an kashe mutane fiye da 140 a hare-haren bam na kungiyar Boko Haram a arewacin Najeriya kama daga watan janairun wannan shekara. Kungiyar ta Amnesty ta ce su ma ‘yan sanda sun kai hare-haren da suka yi sanadiyar mutuwar mutane a lokacin da suke mayarda martani ga kashe-kashen, ta kuma yi kira ga bangarorin biyu da su kawo karshen wannan tashin hankali.

XS
SM
MD
LG