Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Neja Ta Bada Sanarwar Rasuwar Tsohon Gwamnan Jihar Abdulkadir Kure


Gwamnan jihar Neja na yanzu Alhaji Abubakar Sani Bello

Gwamnatin jihar Neja ta bayar da sanarwar rasuwar tsohon gwamnan jihar Injiniya Abdulkadir Kure jiya Lahadi kuma tuni ta ayyana zaman makokin kwanaki uku a duk fadin jihar

Allah ya yiwa tsohon gwamnan jihar Neja Injiniya Abdulkadir Kure rasuwa a kasar waje jiya Lahadi

Kwamishanan yada labaran jihar Mr. Jonathan Batsa shi ya fitar da sanarwar wada kuma shi ya sanya mata hannu. Gwamnatin jihar ta bayyana rasuwar tsohon gwamnan a matsayin wani babban rashi ga kasar.

Za'a yi zaman makoki na kwana ukku a duk fadin kasar har zuwa ranar da za'a kawo gawar marigayin .

Ranar da za'a kawo gawar gwamnatin jihar tace babu aiki domin a karrama mamacin da kuma ba kowa damar kasancewa wurin jana'izar.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

XS
SM
MD
LG