Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijar Ta Musanta Zargin Yin Amfani Da Sarakuna


Shuwagabannin Najeriya da Chadi, Nijar dakuma Kamaru Zasu Yaki Boko Haram, Oktoba 9, 2014.

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta musanta zargin da ‘yan adawa ke yi na cewa shugaba Issoufou Muhammadou na amfani da sarakuna wajen yin kamfe domin ta lashe zabe mai zuwa.

Ministan sadarwar kasar Yahuza Sadisu ne ya bayyana hakan a wata ganawa da ya yi Muryar Amurka.

A farkon makon da ya gabata ne ‘yan adawa a kasar suka yi zargin cewa Issoufou na amfani da sarakunan na gargajiya domin samun nasara a zaben da ke tafe.

A ranar 21 ga watan Fabrairu ake sa ran za a yi zaben shugaban kasa a zagayen farko.

A kuma jiya Asabar ne aka kaddamar da yakin neman zabe a duk fadin kasar inda ‘yan takara za su shiga sako-sako domin neman kuri’u.

A can baya ma ‘yan adawan sun zargi shugaba mai ci da fara gudanar da yakin neman zabensa kafin a kaddamar a hukumance.

Domin jin martanin da gwamnatin ta mayar game da zargin yin amfani da sarakunan gargajiya da ‘yan adawa suka yi, saurari jawabin ministan sadarwa Yahuza Sadisu:

please wait

No media source currently available

0:00 0:00:29 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG