Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijar Ta Tsawaita Dokar Ta Baci A Yankin Diffa


Shugaban Nijar Mahammadou Issoufou

Tun lokacin da kungiyar Boko Haram ta soma kai hare-hare a yankin Diffa gwamnatin kasar Nijar to soma kafa dokar ta baci ta wata ukku ukku wadda yanzu ma ta sake sabuntawa ta wani wata ukkun ta ga abun da hali yayi.

Ganin irin illar da cigaba da tsawaita dokar ke yiwa zamantakewar jama'ar yankin ya sa Muryar Amurka ta zanta da Farfasa Isuhu Yahaya malamin Jami'ar Yamai mai sharhi akan alamuran tsaro.

Farfasa Isuhu yace akan san ranar da za'a fara yaki amma ba'a san ranar da zai kare ba saboda haka tsawaita dokar ta baci a yankin Diffa abu ne da ya zama dole. Tsawaita dokar tamkar karin iko ne aka ba sojoji su samu su gama aikin da aka basu. Dokar ta bada izinin nemo bakin zaren warware matsalar da ta addabi yankin na Diffa.

Farfasa Isuhu yace sai an kai inda 'yan ta'adan suka yadda a tattauna dasu kana a soma batun takaita dokar ta baci. Amma yanzu ba'a kai wannan matsayin ba, inji Isuhu. Aikin sojoji ne su tabbatar 'yan kasa sun zauna lafiya.

Dangane da ko tsawaita dokar nada illa ko haddasa koma baya ga alamuran yau da kullum na zamantakewar jama'a sai Farfasa yace dole ne ya shafi jama'a ta yadda basa so saboda duk inda aka sa dokar ta baci zaman lafiya ne ya tabarbare. Mutane su gane cewa an kafa dokar ta bacin ne domin a samu mafitar dawo da zaman lafiya.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG