Jiya Litinin Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry ya isa London, zangonsa na biyu a ziyararsa ta karshe a wannan mukami.
Birtaniya wacce take cikin masu sukar lamirin gwamnatin Amurka mai barin gado, shugabannin Britaniya kusan sun ma manta da gwamnatin hankalinsu yana kan gwamnati mai zuwa ne.
Ganawarda Mr. Kerry yayi da Sakataren Harkokin Wajen Britaniya Boris Johnson, ya maida hankali ne akan Syria da wasu batutuwa. Haka nan Kerry ya gana da babban Bishop na kasar Ingila Justin Welby, inda shugabannin biyu suka tattauna kan bukatar kasa da kasa su maida hankali akan neman sulhu.
Gwamnatin Ingila jiya Litinin ta fi maida hankali ne kan kalaman shugaban na Amurka mai jiran gado inda ya bayyana goyon bayansa ga ficewarIngila daga kungiyar Tarayyar Turai, da kuma tabbacin da sabuwar gwamnatin Amurka tayi cewa Ingila ta tsammaci sabuwar yarjejeniyar cinikayya tsakanin kasashen biyu.