Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BURKINA FASO: Gwamnatin Ouagadougou Ta Bada Hutun Makokin Harin Da Aka Kai Musu


Wani Bangare Na Harin Otal Din Splendid, Burkina Faso
Wani Bangare Na Harin Otal Din Splendid, Burkina Faso

A makon da ya gabata ne dai aka kai mummunan hari a Burkina Faso da yayi sanadiyyar asarar rayukan mutane da jikkata da dama awani katafaren Otal mai suna Splendid da ke Ouagadougou, babban birnin kasar.

Burkina Fasa ta bada hutun kwanaki 3 a duk fadin kasar na makokin mutane 29 da suka mutu ‘yan kasashe 18 a mummunan harin da aka kai a wani babban Otal mai suna Splendid da ke babban birnin kasar.

Wadanda suka mutu a harin sun hada da wasu ‘yan kasar Canada guda 6, da ‘yan Faransa guda 2, da ‘yan Siwizilan guda 2 da kuma wani Ba’amurke guda 1. Sai kuma mutane da dama da suka jikkata.

Shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore da ya fara mulkin kasar a watan da ya gabata yace, bayyana cewa, a karon farko kasar ta sami fadawa jerin munanan hare-haren da ake kaiwa a duniya.

Kungiyar ta’addar Al-Qaida Maghreb ne suka dau alhakin kai harin.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG