Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Spain Ta Bukaci Kotun Koli Ta Bada Iznin Kama Madugun 'Yan Aware


Madugun 'yan awaren Vatalonia Carles Pudgemont
Madugun 'yan awaren Vatalonia Carles Pudgemont

Masu shigar da kara a Spain sun yi kira ga kotun kolin kasar da ta farfado da sammacin neman a kama tsohon shugaban yankin Catalonia, Carles Puigdemont.

A halin yanzu Puigdemont yana Denmark inda zai yi wata muhawara akan Catalonia a Jami’ar Copenhagen a ranar Litinin din nan, kuma zai gana da ‘yan majalisar Denmark gobe Talata.

Ba’a tabbatar ba ko alkalin kotun kolin Pablo Llarena, wanda ke kula da karar zai amince da hakan ba.

Gwamnatin Spain ta yi barazanar bada sammacin a kama mata Puidgemont idan ya bar Belgium inda ya tsere domin guje wa fuskantar hukunci akan rawar da ya taka a neman ‘yancin Catalonia a watan Oktoban da ya gabata.

Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG