Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Taraba Ta Kare Kanta Akan Kafa Shingayen Tantance Masu Shiga Jihar


Gwamnan Jihar Taraba Arch. Darius Dickson

akawanakinn baya ne gwamnatin jihar Taraba ta dauki matakan yin anfani da shingaye tana tantance duk wanda zai shga kihar lsmsrin ds mutane da dama yin tur da sfirin amma yanzu tace tayi hakan ne sanoda hana bata gari shiga jihar

Gwamnatin jihar Taraba ta kare kanta daga sukar da a keyi mata da kafa shingaye don tantance karuwar yawan baki da ke kaura zuwa jiha da cewa tana yin haka don gundun masifu da jihohi makwabta ke fama da su na ta’addanci da sace-sacen jama’a.

Wakilin Muryar Amurka Sanusi Adamu ya yi hira da gwamnan jihar Taraba Arh, Darius Dickson Ishaku inda ya tambaye shi gaskiya ne matakan da ya dauka na tankade da rairayar baki da ke shiga jihar ba wata hanya ba ce ta nunawa baki da ke matsayinsu na ‘yan Najeriya kyama ba.

Gwamnan ya ce jiharsa ta kadu ganin irin tashe tashen haukula da sace mutane don neman kudin fansa da ke aukuwa a sauran jihohi makwabta sakamakon haka ne ma suka kafa shingaye don gudun bata gari da kuma ragowar ‘yan Boko Haram da ke tserewa daga yaki da sojojin Najeriya daga mabuyarsu na gandun dajin Sambisa shiga jihar. A cewarsa yanzu haka masu sukan matakin sun soma ganin fa’idarsa na rashin ayukan ta’addanci da raguwar sace mutane da jiha ke cin moriyar ta.

Jihar Taraba inji gwamna Arch. Darius Dickson Ishaku tana sane cewa babu wata jiha da zata samu bunkasa ta tattalin arziki ba tare da mu’amala da karbar baki ba, amma ya ce tilas ta yi taka tsantsan wajen lura da halayyar masu shiga jiha don kare lafiya da tabbatar da tsaron jama’a. Yana mai nuni da abinda ya kira sakaci na hukumomi da kula da iyakokin Najerya na daga cikin dammar da Boko Haran ta samu na daukar mayakanta da akasarinsu ‘yan kasashen makwabta ne.

Ga karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Facebook Forum

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Marigayi TB Joshua
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Gidajen Rediyon Najeriya Sun Gana Da Jami'an Diplomasiyya Kan Rikicin Twitter
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG