Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya ta sake salon yaki da cutar Polio


Ana ba wani yaro maganin rigakafin shan inna
Ana ba wani yaro maganin rigakafin shan inna
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa, ta gane kuskuren da take yi a yaki da cutar shan inna da ya yi sanadin shawo kan cutar ta kuma dauki matakan gyara.

Ministan lafiya farfesa Onyebuchukwu, Chukwu wanda ya bayyana haka, yace, sakamakon darasin da gwamnatin tarayya ta koya, ta gabatar da wadansu sababbin dabaru da suka hada da amfani da na’urar sa ido kan dukan lungun da ma’aikata suka shiga domin yiwa yara rigakafi, da kuma sa ido kan masu kaura daga wuri zuwa wuri a yankunan da aka fi fama da cutar.

Ministan ya kuma bayyana cewa, za a dorawa jami’an gudanar da allurar rigakafi alhakin duk wani koma baya da aka samu a yankunan da suke aiki.

Farfesa Chukuwa yace shugaba Goodluck Jonathan ya kuduri aniyar shawo kan cutar kafin shekara da dubu biyu da goma sha biyar da kasashen duniya suke kyautata zaton cimma muradun karni.

Ya kuma yabawa cibiyoyi masu zaman kansu da kungiyoyin aikin jinkai da suka hada da asusun tallafawa kananan yara na UNICEF da gidauniyar Bill da Milinda Gates da gwamnatin kasar Japan da kuma Hukumar lafiya ta Duniya domin rawar da suke takawa da mara baya na ganin nasarar shirin.

Najeriya har yanzu tana daya daga cikin kasashe uku da ake ci gaba da samun yaduwar cutar inda a cikin shekarar nan, aka sami kananan yara dauke da cutar a wadansu jihohi kamar Kaduna da Niger inda ake kirarin shawo kan cutar a shekarun baya.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG