Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Kuduri Anniyar Kwato Kayayyakin Tarihinta Da Aka Sace Zamanin Mulkin Mallaka


MInistan yada labarai Lai Mohammed

Ministan yada Labarai Lai Mohammed ne ya bada wannan tabbaci a wani bikin nuna kayan tarihin kasar da aka kwato daga kasashen ketare.

Ministan yada Labarai na Najeriya Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana kudurin gwamnatin tarayyar kasar na ci gaba da fafutukar ganin ta kwato dukkan kayayyakin tarihi da aka sace daga kasar zamanin mulkin mallaka zuwa kasashen waje.

A jawabinsa Minista Mohammed, ya gayawa mahalarta bikin nuna kayyakin tarihi da aka yi a Legas cewa, gwamnati tana basu tabbacin cewa ba zata yi kasa a guiwa ba wajen ganin dukkan kayyakin tarihinta da aka kai kasashen yammacin duniya da kuma Amurka an dawo da su.

Ita ma a nata jawabin wata 'yar kasar Amurka Malama Jeane, wacce take karantar da kayayyakin tarihi a jami'ar Benin, ta bayyana takaicin ganin 'yan Najeriya basa sha'war karatu kan dadaddun kayan tarihi, sun gwammace na zamanin yau.

Shugaban hukumar da take kula, da kuma adana kayayyakin tarihi Alhaji Yusuf Abdullahi Usman, yayi karin haske kan kasashe shida ciki harda Amurka da Faransa, wadanda suka maidowa Najeriya kayayyakin tarihinta.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG