Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayya Ta Raba Gidan Sauro Miliyan 1.9 A Jihar Delta


Wani ya kwanta cikin gidan sauro mai magani

Kwamitin kasa kan yaki da zazzabin cizon sauro yace za a raba gidan sauro mai magani miliyan 1.9, domin yaki da cutar zazzabin cizon sauro a duk fadin jihar Delta.

Kwamitin kasa kan yaki da zazzabin cizon sauro yace za a raba gidan sauro mai magani miliyan 1.9, domin yaki da cutar zazzabin cizon sauro a duk fadin jihar Delta.

Kwamitin yace, za a raba gidan sauron a dukan gidajen dake shiyoyin mazabun majalisar dattijai uku na jihar.

Da yake Magana a Asaba, babban birnin jihar, a farkon shirin, Godson Kingsley shugaban kungiyar, yace, yakin ya kunshi kashe kwayoyin sauron, da tsabtace muhalli.

Ya bayyana cewa, an girke duba gari 25 a kananan hukumomi, da gefen kogi, domin kiyaye bata gari. Bisa ga cewarshi, ”anyi kowanne shiri domin kiyaye aikin malaman asibiti da ‘yan siyasa daga kwashe gidajen sauron. Bayan nan, akwai jami’an da zasu ci gaba da shirin 18, da zasu yi aiki a kowanne sashi na jihar, yayinda wadansu mutane 100 masu zaman kansu zasu yi aiki domin tabbatar da ganin gidan sauron a isa ga masu amfani da shi”.

Ya kara da cewa, gwamnatin tarayya tana son a raba kashi 97% na gidan sauron, ko kuma dukanshi a yunkurin rigakafin da aka fara da jihohi 31. Ya kuma yi gargadin cewa kada a rika shanya domin kada a rage karfin maganin dake jiki.
XS
SM
MD
LG