Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatoci Najeriya Sun fara Janye Daukar Nauyin Aikin Hajji


Wadansu gwamnatocin Najeriya sun bi sahun jihohin Kaduna da Nassarawa wajen bayyana niyar janye daukar nauyin zuwa ayyukan ibada na Musulmi da Kirista.

Wadansu jihohin sun soke wannan al’ada da kuma rage yawan jami’an da ake turawa domin kula da jin dadin masu ayyukan Ibadan.

Masu kula da lamura a harkokin ayyukan hajji sun bayyana goyon bayan daukar wannan matakin da suka ce, yana tauye ci gaban jihohin inda ake karkatar da kudaden da ya kamata a yiwa al’umma ayyukan jin dadin rayuwa kamar gina asibitai, wajen daukar nauyin aikin hajji domin siyasa abinda suka ce ba daidai bane.

Banda haka kuma, wadansu akan basu kujerun siyasar basu da halin cin yau balle na gobe, wadanda ya kamata a taimaka masu su sami abinci, yayinda wadansu kuma suke sayar da kujerun da aka basu su sami kudi.

Kamfanonin jiragen sama da suka saba jigilar alhazai sun bayyana kamala shirin jigilar alhazai kamar yadda suka saba.

Ga cikakken rahoton da Nasiru Adamu el-Hikaya ya aiko daga Abuja, Najeriya.

Rahoton aikin hajji-2:06'
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:06 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG