Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnonin Arewa Sun Yi Kiran A Soke Kwangilolin Titunan Da Ba a Karasa Ba


Taron Gwamnonin Arewa
Taron Gwamnonin Arewa

Gwamnonin shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya sun yi kira ga gwamnatin tarayya, da ta kwace ayyukan da aka ba 'yan kwangilar da suka kasa ci gaba da gudanar da su domin a bai wa wadanda za su iya aikin cikin dan kankanin lokaci don ci gaban al’ummar yankin.

Kungiyar gwamnonin sun yi wannan kiran ne a wani taron gwamnonin shiyar arewa maso gabas da suka gudanar a garin Maiguduri na kwana biyu.

Taron ya sami halartar Gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ne ya jagoranci taron, ya kuma karanta wa manema labari jawabin kungiyar gwamnonin inda ya ce, sun yaba wa gwamnatin tarayya tare da rundunar sojin kasar a bisa yakin da suke yi da kungiyar Boko Haram.

Sai dai sun yi kira ga sojojin da su kara kaimi wajen tabbatar da tsaro a yankunan da suke fama da tashe-tashen hankula.

Kungiyar gwamnonin ta kuma yi kira ga ma'aikatar albarkatun ruwa ta tarayya da ta tabbatar da an mai da hankali sosai wajen jan ruwan yankin tafkin Chadi wanda al’umma da yawa ke amfani da shi.

Sannan sun bukaci da a samar wa 'yan sanda makamai na zamani domin taimakawa sojoji wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Gwamnonin sun yi alkawarin yin aiki tare domin ci gaban al’umarsu musamman wajen gano ma’adanan karkashin kasa, kamar su man fetur, iskar gas, harkokin noma da masana’antu.

Sannan sun yi alkwarin hada kai da gwamnatin tarayya wajen habaka makarantun tsangaya da karfafa karatun Islamiyya da na zamani da kuma hana yawon barace-barace.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG