Accessibility links

Hada-hadar Hannayen Jari Daram - inji Jami'an Najeriya


Ngozi Okonjo-Iweala Ministar Kudin Najeriya

A jajiberen soma taron tattalin arzikin duniya da za'a yi a Abuja jami'an kasar Najeriya suna sake jaddada cewa hada-hadar kasuwar hannayen jari na nan tana cigaba duk da hare haren bamabamai kusa da babban birnin.

Gaf da soma taron tattalin arzikin duniya, jami'an Najeriya na sake jaddada cigaban hada-hadar kasuwar hannayen jari duk da hare-haren bamabamai da aka kai akan Nyanya kusa ba babban birnin kasar.

Jami'an sun ce tashin bamabamai da suka hallaka rayuka da sace dalibai mata kusa da dari uku a arewa maso gabashin kasar basu shafi kasuwar hada hadan hannayen jari ba a kasar. Wannan na zuwa ne gaf da fara taron tattalin arziki na duniya a Abuja ranar Laraba mai zuwa.

Ahmadu Manu wani jami'in kasuwar hannayen jari a Abuja yace duk rashin tsaron da ake ciki bai shafi cibiyar kasuwar hannayen jari ba da suke Abuja, Legas, Kaduna da ma Fatakwal kodayake idan akwai rashin tsaro a wani yanki abubuwan rayuwa dake fitowa daga yankin ba zasu fito ba. Abun mamaki Ahmadu Manu yace duk wanda yake son ya saka jari a kasuwar yanzu ne ma lokacin yin hakan. Kamfuna da ake sayen hannayen jarinsu suna nan daram sai ma habaka suke yi. Abu daya da ka iya kawo ja baya shi ne rashin sa hannu ga kasafin kudin kasa. Mutanen waje na zuwa su saka jari su ci riba kana su janye su koma kasarsu, wasu kuma su shigo. Haka kasuwar take tafiya.

Ministan Labarun Najeriya Labaran Maku yace Najeriya ta kama hanyar kamo manyan kasashe da suke gaba a kan tattalin arziki. Yace idan an samu zaman lafiya cikin shekarau biyar ko goma kasar zata kasance cikin kasashe 20 da suka fi girman tattalin arziki a duniya.

A wani gefen kuma 'yan kasuwan canji na Najeriya suna son sauya dabarun sayar da kudaden waje bisa tsarin zamani. Mohammed Bashir jagoran kwamitin amintattun kungiyar 'yan canji yace kotu tace su gudanar da zabe kuma zasu yi hakan nan da sati uku.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
XS
SM
MD
LG