Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadakar Kwamitocin Kasafin Kudi Na Majalisun Najeriya Sun Zauna A Bainar Jama'a


Hadakar kwamitocin kasafin kudi na majalisun Najeriya

A karon farko kwamitocin kasafin kudi na Majalisar Waikilai da Majalisar Dattawa sun zauna a bainar jama'a domin jin bahasin mutane dangane da ayyukan da suke so a yi masu

Hadakar kwamitocin kasafin kudi sun bude dandali akan kasafin kudin bana wanda har yanzu ba'a amince dashi ba watanni biyar bayan da Shugaba Muhammad Buhari ya gabatar dashi ga majalisun.

To saidai har yanzu ana ci gaba da yin anfani da kasafin kudin shekarar 2017 ne wai saboda faduwar tattalin arzikin kasar.

Sanata Abu Ibrahim ya yi nazarin abun da majalisar ta fuskanta bayan an gabatar mata da kasafin kudin. Ya amince cewa an kawo kasafin da wuri amma an nun masu ministoci da yawa basu bada hadin kai ba. Duk abubuwan da aka ce su kawo basu kawo ba. Kwaimotoci kuma ba zasu iya ci gaba da ayyukansu ba sai sun ji daga ministoci da wasu shugabannin kwamitocin gwamnati. A cewarsa abubuwan da suka kawo masu cikas ke nan.

Inji Sanata Ibrahim yin nazarin kasafin kudin a bainar jama'a zai nuna wa jama'a inda matsalar take saboda majalisun da bangaren zartaswa duk aikin jama'a su keyi. Dandalin zai ba kowa damar ya yi magana a san inda matsalar take. Duk inda gyara yake sai a yi.

Daya daga cikin wakilan kungiyoyi masu zaman kansu da suka halarci zaman Kwamred Isa Mustapha wanda ya fito daga jihar Jigawa ya bayyana yadda suke kallon sabon salon da majalisar ta fito dashi. Injishi wannan salon na da mahimmanci domin ba dominsa ba ba'a za'a ga ayyukan gwamnatin tarayya ba a kananan hukumomi. Amma a cewarsa ayyukan da ake yi ana yi ne ba tare da jin yawun al'umma ba dangane da bukatunsu. Ya ce wani sailin sai a ga ayyuka biyu ko uku iri daya a gari guda wanda kuma wasu garuruwan suna bukatarsa. Yakamata a saurari bukatun mutane kana a sakasu cikin kasafin kudin.

Shi ma shugaban kwamitin kula da kasafin kudin a majalisar wakilai Mustapha Bala Dawaki ya ce bin digdigin kasafin zai yi alfanu tunda har an fara gano inda aka sa kudi masu yawan gaske. Yakamata 'yan kasa su zo su fadi ra'ayinsu game da abun da suke bukata da kuma abubuwan da suka gani cikin kasafin. Idan akwai gyara su bayyanawa jama'a. Anal misali sun gano kusan Nera biliyan daya na share ofishin mai ba shugaban kasa shawara akan tsaro.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG