Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadarin mota a Hanyar Ibadan ya Hallaka Mutane da Yawa


Mummunan hadarin mota ya kashe mutane da dama wasu kuma sun jikkata, a kan hanyarsu daga Lagos zuwa Kano.

Wani mummunan hadarin mota yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama a kan hanyar garin Ibadan kusa da garin Akinyele dake jihar Oyo.

Wasu shaidun gani da ido sun fadi cewa wata motar zamani kirar Bos ce tayi hadarin kuma mutane shidda sun mutu, tara kuma sun sami raunuka. Ya kuma kara da cewa sun yi kokarin tuntubar iyalai ko dangin wasu daga cikin wadanda suka mutu amma basu yi nasara ba. Yanzu haka dai wasu na asibiti.

Motar ta tashi ne daga unguwar Alaba, jihar Lagos akan hanyarta zuwa Kano yayinda hadarin ya faru a daren jiya da missalin karfe 10 da rabi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

XS
SM
MD
LG