Ganin yau itace jajibirin zaben shugaban kasa a Najeriya, hakan yasa mun gayyato wasu shuwagabannin addinai, don su kara fadakar da al’umah dan gane da hadduran rashin bin doka da oda, a lokacin da bayan zabe. Bakin sune Mr. Bejida Malik da Sheik Ibrahim Duguri.
Sun yi kira kamar haka. Mr. Malik, ya fara da cewar hukumomi masu ruwa da tsaki su tabbatar da cewar sun yi adalci a lokacin gudanar da wannan aikin, ai yi kokarin bama kowane dan kasa damar ya kada kuri’ar shi ba tare da wani muzgunawa ba a lokaci da bayan zabe.
Ita kuma hukumar zabe me zamankanta, ta tabbatar da cewar ta yi aiki yadda yakamata kuma a fadi sakamako yada al’umah suka kada kuri’arsu, batare da wani magudi ba. Ta bakin shi kuwa Shiek Ibrahim Duguri, kuwa yabayyanar da cewar, duk abun da ke kawo wadannan matsalolin, ba wani abu bane illa shuwagabanin da ke hayewa karagar mulki sukan kasance ba wadan da mutane ke zaba bane, don haka idan sun kai ga wannan mukami zakaga cewar basu da wata damuwa ga ‘yan kasa.
Saboda ba tunanin al’umah ne a ransu ba. Babban burinsu shine su kyautata ma nasu da uban gidajensu. Baki daya dai sun yi kira da jama’a su yi kokarin ganin sun fita wajen zabe a loaci da ya kamata, kuma su tabbatar da cewar sun bi dokar hukumar zabe da ta kasa, don samun zaman lafia.