Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Halin Da Kasuwannin Hannayen Jarin Asiya Ke Ciki


Hoton hannayen jarin duniya na kwanakin baya

Kasuwannin hannayen jari sun tashi a yau Litinin bayan da Shugaba Donald Trump ya rattaba hannu a wasu jerin umurni.

Ana sa ran wadannan umurnin za su tsawaita wa’adin shirin tallafi da gwamnati ke ba Amurkawa, domin rage radadin da annobar coronavirus ta haifar

A Asiya, kasuwar hannayen jari ta S&P/ASX ta tashi da kashi 1.6, yayin da ta Shanghai ta yi sama da kashi 0.7.

Kasuwar KOSPI ta Seoul ita ma ta yi sama da kashi 1.4 sannan TSEC ta Taipei ta cilla sama da kashi 0.5.

Da tsakar ranar yau Litinin kasuwar Hang Seng ta Hong Kong ta karu da kashi 0.6 yayin da Sensex ta Mumbai ta yi sama da kashi 0.7.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG