Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hana Hafsan Hafsoshin Indonesia Shiga Amurka Ya Jawo Takaddama Tsakanin Kasashen


Hafsan Hasoshin Indonesia General Gatot Nurmantyo da Amurka ta hanashi shiga kasarta

Takaddamar da ta kunno kai bayan da aka hana babban hafsan hafsoshin sojin Indonesia shiga Amurka, ta jefa huldar da ke tsakanin kasashen biyu cikin tarzoma.

An hana Janar Gatot Nurmantyo shiga jirgin saman kamfanin Emirates zuwa Washington a ranar Asabar a filin tashin jirage na Soekarno- Hatta, yayin da ya kamo hanyarsa ta halartar wani taro kan yaki da ta’addanci a wannan mako, bayan goron gayyata da takwaran aikinsa na Amurka, Janar Jospeh F. Dunford Jr. ya aika masa, wanda shi ne babban hafsan-hafsoshin Amurka.

Tuni dai jakadan Amurka da mataimakinsa a Indonesia suka ba da hakuri kan wannan lamari, wanda ga dukkan alamu ya samo asali ne saboda matsalar da aka samu yayin tantance fasinjoji saboda tsaro.

Sai dai duk haka, wannan matsala ta haifar da nakasu a huldar diplomasiyyar kasasehn biyu domin shugaban sojin na Indonesia ya ki amincewa ya yi tafiyar a wani jirgi na daban da aka tanada masa, bayan abinda ya faru a ranar Asabar.

Izuwa wayewar gari ne kuma alamun nuna kyamatar Amurka suka fara bayyana a birnin Jakarta.

Ma’aikatar harkokin wajen Indonesia ta ce hakurin da Amurka ta bayar bai gamsar ba, inda ministan ma’aikatar Retno Marsudi ya ce “wannan babban al’amari ne mai muhimmanci, saboda haka suna bu

Facebook Forum

An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG