Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hanyoyi Hudu Don Inganta Koyar da Dalibai


Malamai
Malamai

Wani tsohon malami kuma shugaban wata makaranta, a matakin (Principal) a nan Amurka, me suna Mr. Brian Gatens, ya yi wani bincike da ya gano wasu hanyoyi 4 da malamai zasu bi don inganta koyarwar su.

Ya fara da cewar malamai su dauka cewar su aikin su na koyarwa ne ba na kwarewa ba, wannan shine kadai hanyar da zasu kalli wannan sana’ar koyarwar don inganta ta, mafi akasari malamai sukan kalli kansu a matsayin masana kuma kwarraru. Wanda kuwa idan aka duba sai aga akasin hakan.

Idan kuwa malami zasu dinga duba kansu a matsayin 'yan-koyo to bisa ga wannan shi zai sa su bada hazaka wajen inganta koyarwarsu, kadan-kadan, da tabbatar da dalibansu sun samu nagartacen ilimi.

Sai ya fara zayyano wadannan matakan, inda yace na farko shine, malami/malama su dinga kallon yadda malamai yan’uwansu ke koyarwa, wane irin salon tarbiyya suke sama yara a lokkuttan darrussa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG