Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hanyoyin Taimakon Rage Kitse Na Jiki


Abinci mai gina jiki da zai rage kitse a jiki
Abinci mai gina jiki da zai rage kitse a jiki

Kwararru sun bayyana hanyoyin rage kitsen jiki da yake haifar da hawan jini

Likitoci sun bayyana cewa, mutum yana iya kara tsawon rayuwarshi idan yana kula da lafiyarshi ta wajen kula da abincin da yake ci da kuma halin rayuwarshi.
Ga jerin matakan da za a iya dauka na rage kitse a jiki wanda yake iya kaiwa ga mutuwa.
• Cin nama kadan. Ka maida nama ya zama kadan cikin abincinka maimakon ya zama da yawa.

• Ka nemi madara mara mai ko kitse da yawa. Ka rage abinci da ya kunshi nono ko madara mai yawa; maimakon haka, yi amfani da mara kitse da yawa.

• Lura da ciye-ciyen ka. Ka zabi kayan ciye-ciye marasa mai da yawa. A maimakon haka ka rika cin karas , busassun abinci, da ganyaye a madadin masu mai da yawa kamarsu soyayyen dankali.

• Rage mai da ya jike sharaf a girki. Yi amfani da ruwan mai a madadin busashshe.

• Ka rage amfani da manja da mankoko. Yawancin wannan mai yana jike ne, amma yawancin wannan suna dauke da kitse sosai. Yi amfani da man suya, da sauransu.

• Rage abinci mai kitse. Yi kokari kaci abinci dake da mai kasan 200 mg a kowacce rana. Rage cin kwai zuwa guda hudu a sati.

• Ka kara yawan abinci mai bada karfin jiki. Kara abinci mai kawo karfi – kamarsu ‘ya’yan itace da kayan gona, da abinci masu kwaya da ya hada da wake busasshe, da suke da abubuwan Karin karfi

• Kaci ‘ya’yan itace da ganyaye. Domin kiyaye zuciyar ka, kaci ‘ya’yan itace da ganyaye.
Kayi amfani da kwayoyin hatsi. Kwayoyin hatsi na rage cututtukan zuciya. Suna cikin kayan lafiya na jiki, kuma hanyar samun abinci mai gina jiki, amma yi hankali domin suna kawo kiba.

• Kara yawan kifi cikin abincinka. Kasashe masu yawan cin kifi suna da raguwar mutuwa daga kowacce damuwa, haka ma daga cutar zuciya.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG