Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu An Gaza Samar Da Tsaro Mai Dorewa A Kasar Sudan Ta Kudu


South Sudan Rebels Return
South Sudan Rebels Return

Amurka ta bukaci kasashen yankin Gabas ta Tsakiya dasu bayyana rahoton dake kawo wa yunkurin samar da zaman lafiyaa Sudan ta Kudu cikas

Amurka tayi kira ga shugabannin kasashen Gabas ta tsakiya da su fidda rahotannin nan biyar da ba wallafa suba, wanda ke nuna kin bin yarjerjeniyar tsagaita bude wuta da aka cimmawa da kaar Sudan ta Kudu da taki mutuntawa a watan December bara, kana a hukunta duk wanda keda hannu cikin wannan kauce wa wannan matsaya da aka cimmawa.

Wani babban jamiin fadar White House ne ya shaidawa wa wakilin wannan gidan Radiyon haka.

Hukumar ciyar da kasashe gaba na yankin kasashen gabas ta tsakiya, da ake kira IGAD a takaice ta share shekaru 4 tana kokarin ganin anyi sulhu a kasar ta Sudan ta Kudu amma lamarin yaci tura.

Wannan ne ma yasa tayi gargadin cewa zata sa takunkumi na musammam ga kwamandojin dake kara jefa kasar cikin yaki.

Sai dai IGAD din bata aiwatar da wannan barazanar nata ba ko kuma bayyana irin hukuncin da take aniyar dauka ba.

Amma dai kungiyar ta kasashen yankin gabas ta tsakiya ta umurci wani tawagar sojoji daya binciki wannan kin mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wutar a kasar ta asaudan ta Kudu.

Ministan harkokin wajen kasar Habasha,Workneh Gebeyehu wanda ya jagoranci taron na IGAD, yaki yace uffan akan dalilin da yasa kungiyar tasu taki bayyana wannan rahoton nasu a bainar jamaa.

A ranar 26 ga watan Maris dai IGAD ta fitar da bayanin bayan taro, wanda kungiyar tace ta aike wa kungiyar tarayyar Africada kofi guda domi daukar matakin da take ji ya dace.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG