Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ba’a Fara Sayar Mana Da Ɗanyen Man Fetur A Naira Ba - Kungiyar CORAN


Hedikwatar NNPC
Hedikwatar NNPC

Gamayyar kamfanonin tace albarkatun mai a Najeriya (CORAN) sun bayyana cewa har yanzu babu wani mamban kungiyarsu da aka fara sayarwa danyen mayi da kudin Naira.

Sakataren hulda da jama’a na kungiyar Echie Idoko, ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai.

Mista Idoko, ya ce “idan za’a iya tunawa, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya bada umarnin a fara sayar musu da 'danyen mai da kudin Naira, a lokacin wani taron majalisar zartaswa da ya gudana a fadar shugaban kasar, wanda hakan zai taimaka musu wajen samun isasshen mai da zasu tace a kamfanonin su cikin sauki”.

Idoko, ya kara da cewa “duk da wannan sanarwa ta shugaban ƙasa, basu fara cin gajiyar hakan ba, ko da yake akwai bukatar wasu matakai da ka’idodi da yakamata su bi, kafin a fara sayar musu da 'danyen man a Naira”.

Muryar Amurka ta yi kokarin jin ta bakin hukumar kula da albarkatun mai ta ƙasa (NMDPRA) bisa jinkirin fara sayar da 'danyen man a farashin Naira da kungiyar CORAN ta koka akayi, har izuwa haɗa wannan rahoto, hakan ba ta samu ba.

Sai dai mun tuntubi babban mai bincike na kungiyar dillalan man-fetur ta IPMAN Yakubu Ali Bulkadimka, game da tsaikon da matatun mai ke fuskanta wajen fara sayan danyen man a Naira, ya ce “ waɗannan jinkiri da sauran tsaiko da harkar Man-Fetur ke fuskanta a ƙasar, alhaki ne da yake kan hukumar kula da albarkatun mai ta NMDPRA, da kuma rashin tsari na aiwatar da abu cikin lokaci, ya kuma zargi hukumar da rike musu kudaden da suke binta bashi.

Mai sharhi kan lamuran yau da kullum, Nasir Marmara, ya ce jinkirin aiwatar da irin wannan muhimman ayyuka da zai amfani talakan Najeriya ba sabon abu ba ne a kasar, ganin cewa cin hanci da rashawa na tasiri a wasu ma’aikatun kasar.

Masana tattalin arziki irinsu Dr. Isa Abdullahi Kashere, na ganin tafiyar kunkuru wajen aiwatar da ayyukan da suka dace a kasar, yana yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, da kuma ƙarawa talaka kuncin rayuwa.

'Ƴan Najeriya dai na cigaba da koka wa bisa ƙarancin Man-Fetur a kasar da tsadarsa, da kuma tsadar rayuwa.

Saurari cikakken rahoto daga Rukaiya Basha:

Har Yanzu Ba’a Fara Sayar Mana Da Ɗanyen Man-Fetur A Naira Ba - Kungiyar CORAN
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Fim Da Aka Shirya Kan Leah Sharibu Ya Samu Lambar Yabo
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Kalubalen Da Masu Fama Da Lalurar Galhanga Ke Fuskanta
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Tasirin Cibiyar Kula Da Lafiyar Mata Da Yara Ta HopeXchange A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hukumomi Sun Fara Shirin Bada Gudumawar Jini A Fadin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG