Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ba'a San Ko Akwai 'Yan Matan Da Boko Haram Ta Sace A Yobe Ba


'Yan mata 'yan makaranta da 'yan Boko Haram suka sace
'Yan mata 'yan makaranta da 'yan Boko Haram suka sace

Da yammacin ranar Litinin ta wannan makon ne wasu da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram suka kai hari a makarantar 'yan mata dake garin Dapchi cikin jihar Yobe inda wasu 'yan matan suka bace wasu kuma suka samu kubuta

Har yanzu hukumomin jihar Yobe na kokarin tattara adadin 'yan matan dake karatu a makarantar sakandare dake garin Dapchi da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai ma hari yammacin Litinin din da ta gabata.

Tun daga ranar iyaye da abokan arzki suka dinga ziyartar makarantar domin cigiyar 'ya'yansu da wadanda suka sani. Wasu da suka gano 'ya'yansu su na sambarka wasu kuma da har yanzu babu labarin nasu sun mika wa Allah lamarin.

Wannan lamarin yayi kama da harin da aka kai, har aka sace daliban makarantar mata dake Chibok a jihar Borno da aka yi a shekarar 2014.

Alhaji Muhammed Amin kwamishinan ilimi na jihar Yoben a cewarsa ana samun wasu yaran a kauyukan da suka gudu. Amma yanzu ba zasu iya tabbatar da adadin yaran da aka sace ba. Sai dai yanzu gwamnatin jihar ta rufe makarantar.

Wani mahaifin da har yanzu bai san makomar 'yarsa ba ya ce an samu labarin wasu amma tasa babu duriyarta sam. Ya dukufa da rokon Allah Ya dawo da ita gida lafiya.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG