Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Birnin Bouake Na Hannun 'Yan Tawayen Ivory Coast


Mayakan 'yan tawaye da suka tare hanya a Ivory Coast
Mayakan 'yan tawaye da suka tare hanya a Ivory Coast

Wasu manyan birane biyu na kasar Ivory Coast na fuskantar borin wasu tsoffin ‘yan tawaye da aka saka cikin rundunar sojojin kuma aka yi musu alkawarin biyan su wasu kudade da ba’a basu ba.

An ji karar harbe harben bindigogi a yau Litinin a Bouake, birni na biyu mafi girma a kasar da kuma wasu barikokin soji na Abidjan, babban birnin kasar, sai dai har izuwa yanzu babu wani rahoton rasa rayuka.

Yanzu haka gwamnatin Ivory Coast ta kaddamar da shirin kwato biranin Bouake da karfin Soji inda aka kashe wani mutum farin hula jiya Lahadi, yayinda wasu mutane 20 suka jikkata sakamakon bijirewa gargadin ‘yan tawayen na cewa kowa ya zauna gidansa, kada ya fita. Mayakan ‘yan tawayen sun kwace birnin na Bouake a ranar Juma’a da ta gabata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG