Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Kasashen Afirka Na Kan Gaba A Cin Hanci Da Rashawa


Alkaluman cin hanci da rashawa a sassan Afirka.
Alkaluman cin hanci da rashawa a sassan Afirka.

Kasashen Afirka na cigaba da jagoranci a fagen cin hanci da rashawa a duniya.

Kasashen Afirka da dama na daga cikin na baya-baya a jerin kasashen da su ke yaki da cin hanci da rashawa a mizanin rahoton shekara shekara na Kungiyar Yaki Da Almundahana ta kasa da kasa ta Transparency International.

Kasar Somaliya na daya daga cikin kasashen da su ka fi samun yabo mafi kankanta a wannan rahoton da kungiyar ta yaki da almundahana ta fitar a yau dinnan Talata.

Mizanin rahoton ya bai wa kowace kasa maki tsakanin sifili zuwa 100. Baya ga kasar Somaliya, kasashen Afirka da su ka sami maki 20 ko kasa da haka sun hada da Sudan ta Arewa da Sudan ta Kudu da Guinea-Bissau, da Equatorial Guinea, da Chadi da kuma Iritrea.

Kasashen Afirka uku ne kadai su ka sami makin da ya dara 50- kuma su ne Botswana, da Cape Verde, da kuma Rwanda.
Kungiyar ta Transparency International ta ce Afirka ta dan cigaba a ma’aunin habbakar dan adam da kuma tattalin arziki. To amma wannan kungiyar mai hedikwata a Berlin ta ce an ga tabarbarewar gaske ta fuskar kare lafiyar jama’a da batun bin doka da oda.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG