Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Nelson Mandela Na Asibiti


Motar daukan marasa lafiyar da ke dauke da Nelson Mandela

Tsohon shugaban kasar Afirka Ta Kudu Nelson Mandela na cikin tsananin ciwo kuma ya na ci gaba da jinya a wani asibitin birnin Pretoria

Har yanzu tsohon shugaban kasar Afrika Ta Kudu Nelson Mandela ya na asibiti cikin hali mai tsanani, a Pretoria ana ci gaba da yi mi shi maganin ciwon huhun da ya komo mi shi.

Wani kakakin gwamnatin kasar Afirka Ta Kudu ya ce tun da aka sake kwantar da Mr.Mandela da jijjifin jiya asabar, shi da kan shi yake numfashi, wato ba da taimakon wata na’ura ba.

Ofishin shugaba Jacob Zuma ya gabatar da sanarwar cewa jumma’a cikin dare ciwon Mr.Mandela ya tsananta, sannan aka dauke shi daga gidan shi zuwa asibiti.

Nelson Mandela a asibiti
Nelson Mandela a asibiti


Nelson Mandela, Gogarman yaki da akidar wariya da bambancin launin fata, zai yi shekaru casa’in da biyar ranar goma sha takwas ga watan gobe na yuli, kuma a cikin watan afrilun da ya gabata ma ya yi jinyar ciwon madaukai har tsawon kwanaki goma.

Mr.Mandela ya fara fama da ciwon huhun ne tun lokacin zaman kason shekaru ishirin da bakwai da yayi a zamanin mulkin wariyar launin fata. A ‘yan shekarun nan dai ba a cika ganin Mr. Mandela a bainar jama’a ba, saboda karuwar raunin jiki.
XS
SM
MD
LG