Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare-haren Boma Bomai Sun Kashe Jami'an Tsaron Pakistan


Hare-haren boma bomai guda biyu a arewa maso yammacin Pakistan sun kashe akalla mutane 6 tare da raunata wasu da dama a yau Laraba.

Jami’ai sun ce hari mafi muni ya faru ne a gundumar kabilar Mohmand dake kusa da bakin iyaka da Afghanistan, inda wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa da bom bayan da jami’an tsaro suka hango shi suka kuma yi kokarin taka masa burki.

Harin ya kashe jami’an tsaron Pakistan guda 3 da fararen hula guda 2.

Mahari na biyu da ke tare da na farkon shi kuma aka harbe shi har lahira a lokacin da ya yi kokarin ya tada nakiyoyin da yayi damara dasu.

Wata sanarwar soja ta ce maharan guda biyu sun fito ne daga kasar Afghanistan, sun kuma yi shirin kai hari a kan wani yankin dake kumshe da ofisoshi da wuraren horaswa da gidajen kwana na ma’aikatan hukuma a garin Ghalanai dake yankin tsakiyar kasar Pakistan.

XS
SM
MD
LG