Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hari Kan Musulmi: Kasar Sri Lanka Ta Katse Hanyoyin Sada Zumunta


Sojojin kasar Sri Lanka na kokarin tabbatar da tsaro
Sojojin kasar Sri Lanka na kokarin tabbatar da tsaro

Ganin yadda al'ummar Musulmi tsiraru na kasar Sri Lanka ke shan azaba a hannun 'yan kabilar Sanhalese mabiya addinin Budda, gwamnatin kasar ta katse hanyoyin sada zumunta, wadanda ta nan ne ake shirya tashe-tashen hankulan.

Kasar Sri Lanka ta katse hanyoyin amfani da kafafen sada zumunta don dakile yaduwar tashe-tashen hankula kan al’ummar Musulmi tsiraru, yayin da daukacin wannan tsibirar kasa ta kudancin Asiya, ke cigaba da kasancewa karkashin dokar ta baci.
Shugaba Maithripala Sirisena ya kafa dokar ta bacin ne jiya talata, kwana guda bayan da cincirindon masu bore na kabilar Sinhalese da ke bin addinin Buddah su ka kai hare-hare kan masallatai da dama, da kuma wuraren kasuwancin al’ummar Musulmi a yankin tsakiyar gundumar Kandy. Jiya talata ‘yan kwana-kwana sun gano gawar wani matashi Musulmi wanda ya makale lokacin da wuta ta kama wani karamin kantin mahaifinsa.

Tashen hankalin ya samo asali ne ranar Asabar, lokacin da wani direba dan kabilar Sinhalese ya yi fada da wasu matasa Musulmi a Kandy. Washe gari direban ya mutu sanadiyyar raunukan da ya ji.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG