Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani harin bam ya kashe mutane bakwai da raunana mutane ashirin da shidda a garin Biu dake arewa maso gabashin Nigeria.

Wani harin bam ya kashe mutane bakwai da raunana mutane ashirin da shidda a garin Biu dake jihar Borno arewa maso gabashin Nigeria.

Shedun gani da ido sun shedawa sashen Hausa cewa bam di ya tashi da misalin karfe uku na ranar Alhamis, kuma a ranar ake cin kasuwar wannan gari.

Bam din ya tashi ne kusa da wata kofar shiga kasuwar, wanda hakan yayi sanadin mutuwar mutane bakwai da raunana mutum ashirin da shidda.

Harin yasa matasa a garin suka kara kaimin binciken ababen hawa da kuma daukan kwararan matakan tsaro.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG