Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Gombe: An Yi Jana’izar Mutane 12


‘Yan Boko Haram Sun Sake Abka wa Konduga, Jihar Borno, Fabrairu 12, 2014.

Rahotanni daga Jahar Gombe na cewa an gudanar da jana’izar wasu daga cikin mutanen da suka rasa rayukansu a tagwayen hare-haren da aka kai a wasu tashoshi mota da ke jahar.

Hare-haren na baya-baya nan sun auku ne a tashohin mota na Dadin Kowa da kuma Dukku da ke cikin garin Gombe.

A jiya hukumomi suka tabbatar da muturwar mutane 30 a tagwayen hare-haren da aka kai a tashoshin, lamarin da har ila yau ya yi sanadiyar raunata akalla mutane 105.

Wannan hari na zuwa ne kasa da mako guda bayan wani da aka kai a ranar jajiberin sallah karama a jahar a wata kasuwa wanda shima ya salwantar da rayuka da dama.

Wakilin Muryar Amurka ya ruwaito cewa, an kai tagwayen hare-haren ne da daddare inda bama-bamai hudu suka tashi, biyu a kowace tasha.

“An dauko duk wadanda suke cikin dakin ajiye gawa an yi jana’izarsu, mutane 12 aka yi jan’izarsu, a wannan karon an yi jana’izar ne daban daban, ba kamar yadda muka yi a wancan karon na baki daya ba." In ji wani jam’in ba da agajin gaggawa a Jahar.

Ya kuma kara da cewa tun ajiya aka fara sallaman wasu da suka ji rauni daga asibiti “misali wadanda suke takawa da kafufuwansu, an basu magunguna an musu allurai an sallame su.”

Ga karin bayani a rahoton da wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Muhammad ya hada mana:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG