Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan-Akalla Mutane 15 Ne Suka Halaka A Harin Kunab Bakin Wake.


Iraqis take part in a ceremony as part of the Islamic mourning month of Muharram in the holy city of Karbala.
Iraqis take part in a ceremony as part of the Islamic mourning month of Muharram in the holy city of Karbala.

Maharin ya kara babur d a yake kai ne da babbar motar sojoji waccce take jigilar dakarun kasar.

Daga makwabciyar ta Pakistan kuma, rtahotanni sun ce wani harin kunar bakin wake da aka a maraicen jiya Asabar, a yankin kudu maso yammacin kasar ya halaka akalla mutane 15, ciki harda da sojoji da farar hula, kamar yadda hukumomin kasa r suka yi bayani.

Jami'an kasar da shaidun gani d a ido suka ce maharin yana kan babur ne dankare da nakiyoyi loakcinda ya karawa wata motar sojoji dake jigilar dakarun kasar a Quetta babban birnin lardin Baluchistan.

Fashewar ta auku ne a yankin da yake da tsatstsauran matakan tsaro a birnin. Akalla mutane 32 sun jikkata, kamar yadda ministan harkokin cikin gida na kasar Sarafaz Bugti yayi bayani. Da dama cikin wadanda suka jikkatan suna cikin mawuyacin hali.

Wannan hari dai yana zuwa ne a dai dai lokacind a Pakistan take shirin bikin zagayowar ranar da kasar ta samu 'yancin kai a gobe Litinin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG