Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hatsarukan mota a kasa Cameroon a bana sun kashe sama da mutum dubu 11,002.


Hadarin Mota
Hadarin Mota

'Yan kasar Kamaru sun koka akan yadda ake samun yawan haduarin mota a kasar abinda suka ce kusan kullun mutane sama da 50 ne ke rasa rayukan su sakamakon hadarin mota

Yawan hadarin mota a yawancin hanyoyin kasar Jamhuriyar Cameroon na neman jefa jama’ar kasar cikin halin wayyo ni ALLAH. Musammam ma a irin wannan lokacin da ake ciki da daliban makarantun kasar ke komawa hutu.

A bisa kiyasin da akayi ance mutane sama da 50 ne ke rasa rayukan su a kullum a hanyoyin mota a kasar.

A bana kasar ta Kamaru ta fuskanci hatsarurrukan mota fiye da dubu talatin, a yayinda fiye da mutane dubu goma sha daya ne suka rasa rayukansu a sakamakon hatsururrukan mota

Alamu sun tabbatar da cewa rashin kyawon hanyoyi ne ke haddasa wadannan yawan hadduran, sai kuma direbonin da ake zargi da yin tukin ganganci, ko kuma shan abubuwa masu sa maye kafin su shiga motocin nasu.

Mallam Shaibu na cikin shugabannin kungiyar direbobin jamhuriyar ta Cameroon.

Mallam Shuabi ya yiwa wakilin sashen Hausa Awal Garba bayanin cewa, ba shakka yawan hadari kan ana yawan samun sa a cikin kasar kuma daya daga cikin manya-manyan dalilan dake haddasa wadannan hadduran shine rashin kyawon hanyoyi duk ko da yake gwamnati na kokarin ta.

Yace baya ga rashin kyawon hanyoyin haka kuma sunyi kanana sai kuma direbobi suyi ta sharer gudu ba kakkautawa.

Ga Mohammed Awal Garba da Karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG