Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hazo Ya Janyo Hadarin Motoci A Ibadan


CAMEROON: Hadarin motoci

Mutane da dama sun rasa rayukansu yayinda da dama suka ji raunuka a wani mummunan hadari da ya auku tsakanin garin Akinyele da Ibadan da ya shafi motoci tara.

Wani ganau da Sashen Hausa ya yi hira da shi ya bayyana cewa, hadarin ya auku ne sakamakon wani mummunan hazo da ya hana direbobi ganin motocin dake gabansu. Yace wata karamar mota da ta taho a guje ta shiga bayan wata babbar motar dakon kaya abinda ya janyo hadarin motoci tara.

Yace duk da agaji gaggawa da hukumar kula da haduran motoci ta kasa ta kai, an sami asarar rayuka, an kuma dauki wadanda suka ji raunuka zuwa asibi mafi kusa, wadanda daga ciki akwai wadanda suke cikin mawuyacin hali .

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Hassan Umaru Tambuwal ya aiko daga birnin Badun:

hadarin Motoci a Badun-2:55"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG