Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hillary Clinton ta Soki Jonathan Akan Arewacin Najeriya


Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, tana ganawa da shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya a fadar shugaban a Abuja, alhamis, 9 Agusta 2012.
Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, tana ganawa da shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya a fadar shugaban a Abuja, alhamis, 9 Agusta 2012.

Tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton, ta soki gwamnatin Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan musamman ma akan arewacin Najeriya, tana cewa gwamnatinshi tayi facaka da arzikin man fetur dinta, kuma haka ya saka cin-hanci da rashawa yayi karfi sosai a kasar mai fama da rigingimu.

A kan babbar gidan Talabijin din Amurka mai suna ABC, da take ganawa da ‘yar jarida Robin Roberts, Clinton tayi manyan tambayoyi kuma tayi sukar ingancin shugabanci a karkashin Goodluck Jonathan.

Hillary Clinton tace “gwamnatin Najeriya taki daukan alhakin dake kanta, na kiyaye rayukan kananan yara mata da maza, da ma manya mata da maza, a arewacin Najeriya a shekarun da suka wuce.”

“Dole sai gwamnatin Najeriya ta karbi taimako – musamman na tattara bayanai, da nemo bayanai, da kuma ilimin gane shirye-shiryen ta’addanci. Dole ne sai kwararrun sojojinsu zasu yi amfani dasu wajen wannan yakin, kuma zasu fi tabukar abun arziki idan suka karbi taimakon da ake basu. Najeriya ta yanke shawarwarori marasa kyau, ba shawarwari masu wahala ba,” a cewar Clinton.

Clinton ta cigaba da cewa “Sun yi wasa da arzikin man fetur dinsu, kuma sun bari cin hanci yayi katutu, har hakan yasa suna asarar wasu yankunansu, saboda baza su yanke shawarwari masu wahala ba.”

“Gwamnatin Najeriya taki tunkarar barazanar, domin takalar muhimmiyar matsalar. Maganar gaskiya, dole sai gwamnatin Najeriya ta zage damste wajen kara duka mutanenta, da kuma tabbatarwa duka yara sun samu damar neman ilimi,” a cewar tsohuwar Sakatariyar.

“Dole sai anyi amfani da duk kayan aiki. Dole ne kowa ya ga wannan a matsayinsa. Cin zarafin bil adama ne sosai, kuma hakan na daga cikin ire-iren wahalhalun da mutane a Najeriya da ma wasu sassan Afirka suke fama da su,” ta fada a fusace.
XS
SM
MD
LG