Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hillary Clinton Tace Abokin Hamayyarta Trump Kansa Kawi Ya Sani


Hillary Clinton 'yar takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Demokrat

Yar takarar jami’iyar Democrat a zaben shugaban kasa a nan Amurka Hillary Clinton tayi kashedi ga masu kada kuri’a da su lura da cewa Donald Trump mai takarar a karkashin lemar jam’iyyar Republican a koda yaushe kansa kawai ya sani kuma babu ruwansa da kowa.

A jiya Alhamis ne Clinton take fadar hakan lokacinda taje birnin Greenville na jihar Carolina ta Arewa, daya daga cikin jihohi da dole sai dan takara ya lashesu kafin ya zama shugaban kasa.

Hilary Clinton taceshi dai Trump baya iya zama dole kullum sai ya nemicin mutunci mata da marasa galihu, ga shi kumaya fito fili kuma yana nuna cewa shi mutum ne da ya kamata a yi taka-tsatsan gameda shi.

Mai ba Clinton babban gudunmuwa a wannan yakin neman zaben, shugaba Barrack Obama ya yi mata campaign a jihar Florida,daya jihohin da lashe su ke zama dole.

Shi kuma Donald Trump yaje birnin Jacksonville ne,a nan Florida jiya Alhamis inda ya yi hasashen idan Clinton ta lashe zaben to ko shakka babu za a tsigeta saboda sakwannin emails dinta da kuma zancen gidauniyarsu ta Clinton Foundation a lokacinda take sakatariyar harkokin wajen Amurka.

Uwargidan Trump din, Melania, tayi fitowan farko a wurin taron gangamin mijin nata jiya Alhamis tun bayan babban taron jami’iyar Republican na kasa da aka yi a cikin watan Yuli.

XS
SM
MD
LG