Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hotunan Harin Boko Haram akan Bama, Fabrairu 20, 2014

Wani harin baya-bayannan da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne da ake kira Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya ya kashe mutane 115, inda suka kona gidaje sama da dubu daya da dari biyar, sannan suka lalata motoci misali 400, inji wani wanda yaga abunda ya faru. Wani shugaban gargajiya ya zargi sojoin Najeriya da tsoron yin arangama da ‘yan bindigan. Bayan kona fadarshi da aka yi, Shehun Bama, Kyari Ibn Elkanemi yace gwamanti bata dauki yakar ‘yan bindigan da muhimmanci ba, a yankin daya shafe kaso daya cikin shida na kasar Najeriya, sai dai wajen ya nisanta daga inda ma’adanun gurbataccen man yake, wanda ya saka Najeriya a matsayin na daya wajen samar da man fetur a Nahiyar Afirka.

Domin Kari

XS
SM
MD
LG