Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janar Muhammadu Buhari Yayi Kira ga 'Yan Najeriya su Canza Gwamnatin Najeriya Lokacin Zabe Saboda Sakaci da Mulki


Jnaar Muhammadu Buhari,tsohon shugaban kasa kuma shugaban 'yan hamayya.

Shugaban 'yan hamayya janar Muhammadu Buhari yace baya shakkar gwamnan jihar Borno Kashim Shettima yana fadin gaskiya kan gazawar jami'an tsaro a yaki da suke yi da 'yan Boko Haram.

Janar Buhari wanda ya bayyana amincewa da bayanan da Gwamna Kashim Shettima yayi cikin makon jiya, cewa, da alamun 'yan kungiyar Boko Haram sun fi sojojin Najeriya kwarin guiwa da jajircewa da kuma kayana fada, yace Kashim Shettima shine gwamnan Borno, shine shugaban al'umar jihar, yafi kowa sanin abunda yake faruwa a jiharsa da gwagwarmayar da suke yi na rayuwa.

Janar Buhari yace al'umar da gwamnan yake yiwa shugabanci su ake kashewa, sune ake kona musu gidaje da wuraren kasuwanci da masallatai da majami'u. Kuma baya jin Gwamna Shettima zai yiwa Najeriya kariya ba.

Janar Buhari yace ya zama wajibi ga 'yan Najeriya su dauki mataki lokacin zabe mai zuwa wajen canza gwamnatin tarayya wacce yake ganin kamr ta dauki harkar mulki ko tsaro tamkar wasan kasa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:00 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG