Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Agajin Gaggawa a Birnin Tarayya Abuja na Kira da Azauna Lafiya

Abbas G. Idris, darekta-janar na Hukumar Agajin gaggawa ta Babban Birnin Tarayya, Abuja, a Najeriya
Abbas G. Idris, darekta-janar na Hukumar Agajin gaggawa ta Babban Birnin Tarayya, Abuja, a Najeriya

Hukumomi a birnin tarayya na nuna damuwa dangane da yadda mutane ke tayin tururuwa suna shiga birnin tarayya domin neman mafaka. Mun samu zantawa da Alh. Abbas Idris, shugaban hukumar taimakon gaggawa FEMA ta birnin tarayyar Abuja, a wata ziyara da yakawo ma sashen Hausa a nan birnin washintan.

Yayi muna Karin haske dangane da kokarin hukumar su tare da hadin gwiwa da wasu hukumomin, ta yadda suke taimakama mutane da suke a birnin tarayya, don gudun hijira.

Yace hukumar suna ziyartar mutanen da ke gudun hijira a birnin tarayya da suka kai wajaje 4 wanda kuma suna basu abinci da magunguna, har ma da ilmantar da ‘yayan masu gudun hijira. Kuma dangane da har kar tsaro suna kokarin tantance wadanda suke da bukata na gurin zama, don kada su hade da mugayen mutane. Ya kara da cewar Ministan birnin tarayya ya bada wuri da za’a gina ma mutanennan wurin zama na kankanin lokaci, wanda yanzu haka an fara aikin. Ya kuma yi kira da babbar murya da cewar duk ilahirin mutane su manta da banbancin addini ko kabilanci don neman zaman lafiya da cigaban kasar baki daya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:50 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG