Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar dake Hana Fataucin Mutane Ta Kubutar da Mutane Fiye da Dubu Goma


'Yan Kungiyar BBOG dake fafutikar neman neman yan matan Chibok da aka sace

Fataucin mutane daga kasashe masu tasowa zuwa kasashen da suka cigaba wani abu ne dake ciwa kasashe kamar Najeriya tuwo a kwarya lamarin da ya sa kasar take daukan matakai daban daban da suka hada da kafa hukumar yaki da fataucin mutane domin kawo karshen matsalar.

Darakta Janar ta hukumar yaki da fataucin mutane Mrs Julie Ora Donli ta bayyana irin hobasan da hukumarta ta yi domin kawar da wannan muguwar sana'a da wasu su keyi.

Tace kawo yanzu mun ceto fiye da mutane dubu goma da kuma gurfanar da mutanen dake safarar su 323 gaban kuliya tare da cin nasara. Tace ko a wannan makon sun gabatar da mutane masu aikata aika aikar a jihohin Nasarawa da Edo. Kuma an yanke masu hukumci.

Ganin yadda ake fataucin mutane zuwa kasashen da suka cigaba tace suna aiki da gwamnatocin kasashen irinsu kasar Spain da Italia da Birtaniya da ma Amurka.

Hajiya Halima Baba Ahmed mai fafutikar kare 'yancin mata da yara tace matsalar safarar mutane matsala ce babba kuma tana tada hankali. Tace irin tafiyar ma da suke yi tana da hatsari domin cikin hamada suke bi. Duk wata matsalar rashin ruwa ko abinci da ta taso cikin hamadan nan yawancinsu suke mutuwa. Tace duk da hakan kullum mutane suna yin tafiyar maimakon ma su bi hanyar da doka ta tanada.

Baicin matsalar hamada inji Hajiya Halima akwai ta teku inda sau tari jiragensu ke nitsewa sanadiyar cinkoso ko rashin lafiyar jirgi.

Kwana kwanan nan alkalumma suka nuna cewa 'yan Najeriya sama da dubu hudu suka rasa rayukansu a kogin Baharum lokacin da suke kokarin tsallakawa nahiyar Turai.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG